10 Nuwamba 2020 - 13:08
Shugabannin Kasashen Syria Da Rasha Sun Tattauna Ta Hanyar Bidiyo Daga Nesa

Shugaban kasar Syria Basshar Assad ya yi kira da a kawo karshen kallacewar da aka yi wa kasarsa wanda ba shi bisa doka, domin bai wa gwamnatin ta Syria damar mayar da ‘yan kasarta da ke waje zuwa gida.

ABNA24 : Shugaban na kasar Syria ya kara bayyana cewa; Matsaloli da suke da alaka da mawuyacin halin da ‘yan gudun hijira suke ciki, suna da yawa har yanzu.

Shugaban na kasar Syria ya shaida wa takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin cewa a halin yanzu abu mafi muhimmanci da yake a gaban kasarsa shi ne mayar da ‘yan gudun hijira zuwa gida.

A nashi gefen shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya shaidawa takwaran nasa na kasar Syria cewa; Abinda kasarsa ta sa a gaba a yanzu shi ne ganin cewa zaman lafiya mai dorewa ya dawo a cikin kasar ta Syria.

Har ila yau shugaban kasar ta Rasha ya ci gaba da cewa; Rasha tana goyon bayan taron kasa da kasa da za a yi akan ‘yan gudun hijirar kasar Syria, kuma za ta aike da tawaga mafi girma zuwa wurin taron.

Da akwai ‘yan asalin kasar Syria da suke zaman gudun hijira a waje da su ka haura miliyan shida.

342/